1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kai hari kan gidan yari a kudancin Mali

November 7, 2016

Ba a dai san wadanda suka kai harin ba, amma masu kishin addini sun tsananta hare-hare a Mali cikin wannan shekara.

https://p.dw.com/p/2SJ6P
Al-Kaida im Islamischen Maghreb
Hoto: AFP/Getty Images

Wasu 'yan bindiga da ba a gane su ba sun kubutar da firsinoni 21 a garin Banamba da ke kudancin kasar Mali a daren ranar Lahadi a wani abinda ministan shari'ar kasar ya kwatanta da "harin ta'addanci". Mamadou Ismael Konate ya fada a wannan Litinin cewa maharan su shida sun so su saki wasu 'yan ta'adda biyu amma ya ce tuni an mayar da su wani gari. Ministan ya ce wani gandiroba ya bace bayan harin da 'yan bindiga suka kai, sai dai bai yi karin bayani. Ko da yake ba a san wadanda ke da hannu a harin ba amma a wannan shekara kungiyoyin kishin addini irinsu Ansar Dine sun tsananta kai hare-hare a cikin Mali, inda suka kai hare-hare har guda 60 ciki har da wanda suka kai kan cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da wasu wurare, kana suna kara kutsawa kudancin kasar inda a da ke zaman tudun mun tsira.