1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Birtaniya na kada kuri'a kan batun ficewa daga EU

Gazali Abdou TasawaJune 23, 2016

'Yan Birtaniya miliyan 46 na kada kuri'arsu a zaben raba gardama kan ko kasarsu za ta zama ko kuma ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai ta EU.

https://p.dw.com/p/1JBzY
Großbritannien Wahlen
Hoto: DW/B. Wesel

'Yan kasar Birtaniya na ci gaba da kada kuri'arsu a zaben raba gardama kan ko kasar za ta zauna ko kuma za ta fice daga Kungiyar Tarayyar Turai ta EU. Mutane sama da miliyan 46 ne dai suka cancanci kada kuri'ar tasu a zaben mai cike da tarihi wanda aka bude runfana tun a misalin karfe bakwai agogon kasar.

Gidajen talabijin na kasar sun nuno jerin mutane a runfunan zabe duk da rashin kyakyawan yanayi. Sai dai har ya zuwa wannan rana ta zabe dai 'yan kasar ta Birtaniya na ci gaba da yin waswasi kan zabin da ya kamata su yi tare da dora ayar tambaya kan tasirin da zama ko kuma ficewa daga cikin Kungiyar ta EU zai haifar masu.

Sai dai wani bincike jin ra'ayin jama'a na baya baya ya nunar da cewa masu ra'ayin ci gaba da zaman kasar ta Birtaniya a cikin Kungiyar EU ne ke kan gaba da kashi 52 daga cikin dari. Da misalin karfe10 na dare ne dai za a rufe runfunan zabe wanda ake sa ran bayyana sakamakon nasa da misalin karfe 10 na safiyar Jumma'ar gobe.