1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun fara mika wuya

July 4, 2017

Rundunar sojan Najeriya ta ce 'yan Boko Haram 700 sun shirya ajiye makamakansu. Tuni ma sojoji suka ce wasu 70 daga cikin mayakan sun rigaya sun ajiye makamansu.

https://p.dw.com/p/2fuVU
Boko Haram
Hoto: Java

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa akwai wasu mayakan Boko Haram kimanin 700 da suka zabi ajiye makaman su tare da mika wuya ga rundunar tabbatar da tsaro ta sojojin Najeriya din da ake kira Operation Lafiya Dole da ke shiyyar arewa maso gabashin kasar. A wata sanarwa da kakakin rundunar Sojojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya rabawa manema labarai ta nuna cewa tuni guda 70 daga cikin 700 su ka mika wuya kuma ana kan tantance. Ya zuwa yanzu dai ba wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na sojoji.

Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Iyayen 'yan sanda mata da aka sace na son a kubutar da 'ya'yansuHoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Wannan lamarin dai na zuwa ne daidai lokacin da iyayen matan nan 'yan sanda suka tabbatarwa da duniya cewar da gaske ne an sace mata sabanin abinda rundunar 'yan sanda Najeriya ta furka a kwanakin da suka gabata. A wata ganawa da manema labarai iyayen wanda su kan su na cikin wadan da su ka tsira daga kwanton baunar da 'yan Boko Haram suka yi lokacin da suka sace 'yan sandan sun bukaci hukumomi su gaggauta ceto musu 'ya ya kafin a bin ya yi nisa.

Ya zuwa yanzu dai rundunar 'yan sanda Najeriya din ba ta kai ga cewa komai ba game da wannan bayani da iyayen 'yan sanda suka yi. Su dai matan an sacesu ne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa yi wa wata gawa rakiya a ranar 20 ga watan Yunin da ya gabata inda aka yi awon gaba da 14 daga cikin wadanda dukanninsu 'yan sanda ne.