1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira 18 sun halaka a teku

Gazali Abdou TasawaMarch 6, 2016

Jirgin ruwan da ke dauke da 'Yan gudun hijira ya tuntsire a kusa da gabar ruwan yankin Kudu maso Yammacin Turkiyya. Mutane 18 ne suka mutu, yayin da aka ceto 15.

https://p.dw.com/p/1I8EJ
Armee sucht illegale Migranten in Kolumbien
Hoto: Fuerzas Armadas de Colombia

akalla mutane 18 sun halaka bayan da jirgin ruwan da ke dauke da su a tuntsire a kusa da gabar ruwan tashar shakatawa ta Didim da ke a Kudu maso Yammacin Turkiyya.

Sai dai Jami'an gabar ruwan Turkiyyar sun ce sun yi nasarar ceto wasu 'yan gudun hijirar 15 da ransu da ke a cikin jirgin wanda ke kan hanyar zuwa kasar Girka.

Kuma sun ce yanzu haka sun aika da jiragen ruwa uku da mai dirar angulu guda su na yawo a yankin domin ceto sauran mutanen da ke da sauran kwana a gaba ko kuma gawarwakin wadanda tekun ta ritsa da su.