1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira 30 sun hallaka a Bahar Rum

Yusuf BalaMay 26, 2016

Jirgin 'yan gudun hijirar ya wargaje ne bayan da ya baro gabar tekun Bahar Rum daga Libiya.

https://p.dw.com/p/1Iups
Mittelmeer Libyen Flüchtlingsboot Rettungsaktion
Jirgin da ya kife bayan ya baro gabar teku a LibiyaHoto: Reuters/Marina Militare

Kimanin mutane 30 ne ake fargabar sun hallaka bayan da jirginsu ya jirkice a teku bayan sun baro gabar tekun Libiya, abin da ke zuwa bayan da aka samu dama ta ceton wasu mutanen 'yan gudun hijira kimanin 50 kamar yadda dakarun sojan ruwa daga kungiyar EU suka bayyana a ranar Alhamis din nan.

Kaftin Antonello de Renzis Sonnino da ke magana da yawun dakarun sojan na EU ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa suna tsammanin tsakanin mutane 20 zuwa 30 ne suka mutu a bayanan da jami'ansu da ke aikin yaki da masu fasakaurin jama'a ta teku ke yi a tekun bahar Rum.