1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan gudun hijira a Iraki

July 12, 2007

An samu karuwan yawan yan gudun hijira a bara

https://p.dw.com/p/Btv3
Hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD
Hukumar kula da yan gudun hijira ta MDDHoto: AP

Shekaru biyu a jere kenan ake cigaba da samun karuwar tashe tashen hankula a kasar Iraki,ayayinda dubban alummomin kasar ne ke cigaba da yin gudun hijira zuwa sassa daban daban na duniya sakamakmon wannan tashin hankali.

Rahotan da komitin dake kulawa da yan gudun hijira na duniya ya fitar na nuni dacewa a karshen shekara ta 2006 data gabata ,kusan mutane million 14 ne ke cigaba da rayuwa a matsayin yan gudun hijira,adadin daya karu da kusan million biyu daga na shekarata 2005,wanda kuma ke zama mafi yawa a duk kiyasin da akeyi tun daga shekarata 2001.

Daga cikin mutane miliyan biyu da suka tsere tilas da gidajensu a bara,kusan rabin sun yan kasar Iraki ne,wanda daga cikinsu Amurka ,wadda ke mamayen kasar,ta bawa mutane 202 mafaka a baran,koda yake Washinton tayi alkawarin sake tsugunara da yan Irakin Dubu 3,nan da karshen watan satumba.

Rahotan komitin kula da yan gudun hijiran kazalika ya nunar dacewa ,Syria wadda ke makwabtaka da Irakin,ta karbi bakuncin yan kasar su dubu 450,a bara kadai,wanda ya kawo ga adadin yan Irakin dake kasar zuwa dubu 800,ayayinda Jordan ta karbi mutane dubu 250,wanda ya kawo ga adadin Irakawan dake kasar zuwa dubu 700.Bugu da kari akwai yan kasar ta Iraki budu 80 da suka shiga kasar Masar.

Shugabar komitin kula da yan gudun hijiran Lavinia Limon,ta bayyana cewakamar yadda yakin Irakin ya zame babbar matsala,haka shime batun yan gudun hijiran ya zamanto abu mawuyaci da zaa iya magance shi,domin bashi da ranar kawowa karshe.

Baya ga kasar ta Iraki dai,akwai kuma kasahe kamar Somalia da ake samun sabbin yan gudun hijira sakamakon hare haren da dakarun Habasha suka kaddamar a karshen shekarar data gabata.Dubban yan somalian dai sun shiga kasashen Kenya da Yemen da Habashan domin samun mafaka.B

Bugu da kari Sri Lanka dake fsama da rigingimun yxan tawayen Tamil Tigers da dakarun gwamnati,ya haifar da tserewan yan kasar kimanin dubu 26,zuwa cikin India,domin samun mafaka.

Rahotan ya kuma bayyana cigaban kwararan yan gudun hijira daka rigingimun kan iyaka dake gudana a janhuriyar tsakiyar Afrika ,da Tchadi da Sudan.

Daga cikin adadin yan gudun hijira million 13.9 da ake dasu a duniya baki daya dai,kasa da dubu 70 ne suka samu matsuni na dindin din a shekarar data gabata,inda Amurka ta karbi dubu 41,sai Autralia dubu 12 da 133,canada dubu 10 da 600,kana Sweden dubu 1,555,sai Norway 924,inji wannan rahotan.