1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Gudun Hijirar Afghanistan

November 16, 2004

Sama da #yan gudun hijirar Afghanistan miliyan uku suka koma gida daga kasashen Pakistan da Iran bayan kawo karshen yakin basasar kasarsu

https://p.dw.com/p/Bvea
'Yan gudun hijirar Afghanistan
'Yan gudun hijirar AfghanistanHoto: AP

Da zarar ‚yan gudun hijirar sun sauka filin jiragen saman birnin Kabul za a raba musu kasidun dake kunshe da cikakkun bayanai a game da halin da siyasar kasar ke ciki da kuma barazanar yin tuntube da nakiyoyin da aka bibbinne karkashin kasa, bayan jami'an kiwon lafiya na kungiyar kula da makaurata ta kasa da kasa sun binciki lafiyarsu. Wani da ake kira Georg David daga nan Jamus, wanda yayi kimanin shekaru biyu yana wa kungiyar aiki yayi bayani yana mai cewar:

"A baya ga wasu ‚yan kudade na jari da ake ba su, kazalika makauratan dake komawa gida suna da cikakkiyar dama ta koyan sana’ar hannu da kuma halartar kwasakwasan koyan harsuna ko na’ura mai kwakwalwa. A baya ga haka akwai wata dama ta samun taimakon kudin da ya kai Euro 1.500 domin tinkarar sabon hali na rayuwa da suka shiga."

Daga nan Jamus dai sama da makaurata 400 ne suka tsayar da shawarar komawa gida bayan kawo karshen yakin basasar Afghanistan. Georg David ya ce ‚yan gudun hijirar dake komawa gida suna da kyakkyawar kafa ta samun guraben aikin yi a karkashin matakan sake gina kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita. Akwai wasu dake nuna karfin zuciya wajen bude ‚yan kananan kamfanoni masu zaman kansu. Wasu daga cikinsu ma sun dauki ma’aikata a halin yanzu haka. Georg David ya ba da misali da wani matashin da ya bude kamfanin ciniki da harhada kekuna, wanda daga baya ya dauki mutane biyar aiki. An dai samu ci gaba ma’ana a cikin shekarun da suka biyo-bayan mulkin kungiyar Taliban. An gina sabbin tituna da sabunta gidajen da harsasai suka bannatar, kuma musamman a wannan bangare na gine-gine mutane na da cikakkiyar dama ta samun guraben aikin yi. Dangane da ‚yan gudun hijirar Afghanistan da suka nemi mafaka a nan Jamus kuwa, kawo yanzu, ba wanda ya tilasta musu da su koma gida, illa bisa radin kan mutum. Amma fa bisa ga ra’ayin Georg David a yanzu ne lokaci ya fi dacewa domin komawarsu gida, inda ba a da cunkoson ‚yan gudun hijirar dake komawa gida. Bugu da kari kuma a yanzun ne ayyukan sake gina kasar suka kankama ta yadda mutum zai samu aikin yi a cikin sauki, musamman ga masu jin harsuna irinsu Turanci da Jamusanci domin yi wa kungiyoyi na kasa da kasa aiki. Idan har an samu jinkiri to kuwa murna ka iya komawa ciki dangane da wadanda, daga bisani, zasu yanke shawarar komawa gida. To sai dai kuma har yau kasar Afghanistan na fama da tabarbarewar al’amuran tsaro, inda ake samun hare-haren ta’addanci akai-akai, ko da yake wannan barazanar ta fi shafar baki ‚yan kasashen ketare dake wa kungiyoyi na kasa da kasa aiki.