1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Najeriya na shakkar komawa garuruwansu

Al-Amin Muhammad/ MABDecember 10, 2015

Kungiyoyin farar hula da ‘yan gudun hijrar Najeriya sun nemi shugaba Buhari ya yi taka-tsantsan dangane da matakin da ya dauka na mayar da su garuruwansu a 2016.

https://p.dw.com/p/1HLM1
Nigeria Flüchtlinge vor Boko Haram
Hoto: Reuters/S. Ini

[No title]

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa wata tawagar Kungiyar kula da yan gudun hijira mai suna International Rescue Commitee cewa gwamnati na kokarin kwashe yan gudun hijira daga wuraren da ake tsugune da su zuwa garuruwansu na asali a farkon shekara mai kamawa. Wannan matakin ya biyo bayan saukin alamura da aka samu da kuma kokarin da ake yi na sake gina garuruwa don bada dama ga yan gudun hijirar sama da miliyan biyu komawa yankunan su na asali.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
'Yan gudun hijira na fuskantar matsalar abinci da ruwan shaHoto: Reuters/S.Ini

A martanin da suka bayyana kan wannan batu, ‘yan gudun hijirar sun ce ba za su so komawa yankunansu ba tare da tabbatar da kawo karshen hare-haren yan Boko Haram a shiyyar ba, ganin har yanzu wasu yankunan na hannun mayakan Boko haram. Malam Bukar Bulama daya daga cikin shugabannin yan gudun hijira da ke zaune a nan Gombe, ya ce ba za su koma yankunansu a irin wannan hali da ake ciki ba, har sai an tabbatar da samun cikakken tsaro da isassun jamian tsaro.

Su ma kungiyoyin fararen hula da masharhanta da talakawa suna kira ga gwamnati da ta yi taka- tsantsan don gujewa yin kitso a kan kwarkwata.
Malam Jamilu Dahiru shugaban kungiyar kare hakkin marasa karfi ne a jihar Gombe, ya nemi gwamnatin Muhammadu Buhari ta saurara kan wannan shirin na maida
yan gudun hijirar, har sai an tabbatar da tsaro a yankunansu.

Shugaba Buhari ya yunkura don mayar da 'yan gudun hijira gida
Shugaba Buhari ya yunkura don mayar da 'yan gudun hijira gidaHoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Borno wacce ta kafa sabuwar maaikata don sake gina yankunan ta ce ta na aiki ba kama hannun yaro don sake gina gidajen da jamaa za su zauna a wadannan yankunan. Sai dai har yanzu akwai wuraren da mayakan Boko Haram ke mamaye da su musamman kauyukan da ke bakin gabar tabkin Chadi, abinda ake ganin da sauran aiki na tabbatar da tsaro a yankunan.