1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan Islama a Somalia sun gindaya sharadi kafin su tattauna da gwamnati

July 25, 2006
https://p.dw.com/p/BupB

Shugaban sojojin sa kai na Islama dake iko da Mogadishu babban birnin Somalia ya ce ba zai tattauna batun samar da zaman lafiya da gwamnati ba har sai Habasha ta janye dakarunta daga kasar ta Somalia. Gwamnatin wucin gadin karkashin jagorancin shugaba Abdullahi Yusuf na da mazauninta a garin Baidoa, inda rahotanni suka nunar da cewa sojojin Habasha na tsaron muhimman gine-ginen gwamnati. Gwamnati a birnin Addis Ababa dai na marawa shugaba Yusuf baya, amma ta musanta cewar ta tura dakarunta zuwa Somalia. Da farko dai gwamnati ta amince ta shiga wannan tattaunawa a Sudan, don amsa kiran da MDD ta yi na hana barkewar yaki a wannan kasa dake yankin kahon Afirka.