1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Uganda na musgunawa 'yan jaridu

Kamaluddeen SaniJanuary 11, 2016

Kungiyar kare hakkokin bil -adama ta Human rights watch ta bayyana cewar gwamnatin kasar Uganda na cigaba da muzanta 'yan jarida da masu fadar albarkacin bakin su.

https://p.dw.com/p/1HbZx
Uganda Razzia Medien Protest
Hoto: Reuters

Zargin dai na zuwane a dai-dai lokacin da ake gab da fara zaben shugabancin kasar a wata mai kamawa.

'Yan takarar shugabancin kasar bakwai ne dai suke kokarin bugawa da Shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni da ya shafe shekaru 30 a gadon mulki a ranar 18 ga watan Febreru, a yayin da ake fargabar barkewar rikici a lokutan yakin neman zaben sakamakon sukar lamirin juna kan cin hanci da karbar rashawa a tsakanin 'yan takarar.

Kazalika kungiyar tace gwamnati ta dakatar da wasu aikace -aikacen 'yan jarida tare barazanar daukar matakai masu tsauri ga gidajen radiyon kasar muddin suka dauki nauyin watsa shirye-shiryen 'yan adawar kasar.