1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan kato da gora sun hana kai wani sabon hari a Maiduguri

Salissou Boukari
March 12, 2017

A kokarin da suke na taimakawa a samu tsaro, wasu 'yan kato da gora sun yi nasarar dakile harin kunar bakin wake da wasu 'yan mata guda biyu suka yi niyar kaiwa a Maiduguri.

https://p.dw.com/p/2Z4UX
Civilian JTF
Matasa masu taimakawa wajen samar da tsaro a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP/Abdulkareem Haruna

 A wannan Lahadi ce dai mai magana da yawun 'yan sandan jihar Borno Victor Isuku, ya sanar da wannan labari, inda ya ce 'yan kato da gorar sun yi nasar gano wadan nan 'yan mata ne, wanda hakan ya bai wa jami'an tsaron da ke wurin damar bindigesu tun kafin su tashi bam din da ke jikinsu.

'Yan kungiyar Boko Haram dai na yawan amfani da 'yan mata ko kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake, tun bayan da suka ayyana tashe-tashen hankullan yau shekaru takwas a yankin Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya. Kungiyar kula da ayyukan agaji ta NEMA reshen Maiduguri ta sanar cewa daya daga cikin matan da aka bindige da ke yunkurin kai hari tana dauke da juna biyu.

Mayakan kungiyar ta Boko haram dai sun sace dubban mata da kananan yara, inda daga bisani suna tilastawa da dama daga cikinsu zama 'yan kungiyar, tare da yin amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake a cewar kungiyoyin da ke fafutikar kare hakin dan Adam.