1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara sauraron batun tsige Shugaba Jacob Zuma

Kamaluddeen SaniApril 5, 2016

A ranar talatar nan ce 'yan majalisar Dokokin Afrika ta Kudu suka fara sauraron kudurorin da zasu kai ga tsige shugaban kasar Jacob Zuma daga kujerar mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/1IPQQ
Südafrika Kapstadt Jacob Zuma Präsident
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da babbar kotun kasar ta bayyana cewar shugaban ya keta tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar kashe makudan miliyoyin Daloli wajen yiwa gidan sa garambawul.

Jam'iyyar Democratic Alliance ta adawa a kasar ce ta nemi bukatar a tsige shugaba Zuman bayan da kotun kasar ta ce shugaban ya take ka'ida a makon daya gabata.

To sai dai, Shugaba Jacob Zuman na iya tsallake wannan siradin, a yayin da majalisar Dokokin kasar ke bukatar kashi biyu bisa uku na yawan adadin 'yan majalisar gami da goyan bayan jam'iyyar mai mulki a kasar wato ANC da ke cigaba da mara masa baya kafin a kai ga tsige shi.