1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan majalisar dattawan Amurika sun buƙaci matsa lamba ga gwamnatin Sudan

April 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2m

Mataimakin sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da bada agaji, Jan Egelend, ya yi kira ga kasashendunia da su matsa lamba ga gwamnatinkasar Sudanndominta bada damar kai agaji ga dubunan jama´a na yankin Darfur da ke fama da matsaloli.

Jan Egeland ya yi wannan bayani, a yayin da ya ke maida martani, da haramcin da hukumomin Sudan su ka yi masa, na kai ziyarar gani da ido a yankin Darfur.

Idan ba a manta ba ranar, litinin da ta wuce, gwamnatin Khartum ,ta ƙi baiwa Sakataren, izinin gudanar da rangadi a wanan yanki , da ke fama da yaƙe yaƙe.

Jan Egelabd yayi suka da kakkausar halshe ga gwamnatin kasar Sudan.

Tunni a nata ɓangare, majalissar dattawan Amurika, ta kaɗa kuri´ar amincewa da baiwa gwamnatin shugaba Georges Bush, damar naɗa wakili na mussamman, a ƙasar Sudan da yankin Darfur.

Yan majalisar dattawan Amurika, sunyi kira, ga Majalisar Ɗinkin Dunia, Ƙungiyar tsaro ta NATO, Ƙungiyar gamayya turai, a game da, wajibcin da ya rataya a kan su, na ɗaukar mattakan laddabtar da gwamnatin Sudan , da kuma ceton dubunan rayuka a yankin Darfur.

A ɗaya hannun, sanarwar yan majalisar dattawan Amurika, ta amince da Gwamnatin Bush, ta katse hulɗoɗi, da duk wata ƙasa a wannan dunia, da za ta karya takunkumin cinakin makamai, da aka saka wa Sudan.