1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Niger Delta Avergers sun amince a tattauna

Salissou BoukariAugust 21, 2016

A wannan Lahadin ne mayakan suka sanar da cewa a shirye suke su dakatar da bude wuta, tare kuma da soma tattaunawa da gwamnatin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1JmTD
Nigeria Ölrebellen Pipelines
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Esiri

Hare-haren 'yan kungiyar dai da suka soma tun daga farkon wannan shekara, inda suke neman da ayi adalci, wajen rarraba dukiyar da ake samu ta hanyar man da ake hakowa a yankinsu, sun haddasa koma baya mai yawa ga ayyukan hako man fetir din a Najeriya na wajen ganga dubu 700 a ko wace rana.

Sai dai ana ganin da wuya a samu yarjejeniyar tsagaita buda wuta mai dorewa a yankin, domin akwai ire-iren kungiyoyin 'yan tsagera da dama a yankin masu dauke da makammai. Cikin wata sanarwar dai da suka fitar, mayakan na Niger Delta Avengers sun ce za su ci gaba da yin biyayya ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta kan kanfanonin man kasar.