1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

yan-sama Jannati a Duniyar wata

Abba BashirJanuary 2, 2007

Wace Kasa ce bayan Amurka ta tura Yan-sama jannati Duniyar Wata

https://p.dw.com/p/BvV4
Neil Armstrong a Duniyar Wata
Neil Armstrong a Duniyar WataHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Hassane: Fatawarmu ta wannan makon ta fito ne daga hannun MalamMuazu Isuhu, Yamai a Jamhuriyar Niger. Malamin tambaya ya yi, wai shin, Wace Kasa ce bayan Amurka ta tura Yan-sama jannati Duniyar Wata?

Bashir : Bincike ya tabbatar mana da cewa, ya zuwa yanzu, mutane 12 ne suka aza sawunsu a kan doron Wata.kuma dukkaninsu sun fitone daga kasar Amurka.

Amurka ta fara aikawa da Yan-sama jannati zuwa Duniyar wata a shekara ta 1969, kuma a tsakanin 1969-1972 Amurka ta kaddamar da aniyarta ta aikawa da Kumbo Apollo guda 7 zuwa Duniyar wata wadanda suke dauke da lambobi kamar haka;11, 12, 13, 14, 15, 16, 17. A cikin wadannan jiragen Apollo guda 7, akwai Yan-sama jannati daban-daban har su 21; wato kowanne jirgi yana dauke da mutane 3. Amma dai daga cikin su mutane 12 ne kawai aka hakikance sun taka doron wata da kafarsu.

A kowanne Jirgi, Dan-sama jannati daya yana kasancewa a cikin Jirgi, domin sarrafa Na’ura mai bayar da umarni, a yayin da sauran Yan-sama Jannati 2 ke sauka akan doron wata.Misali a Jirgin Apollo mai lamaba 11 wanda kuma shine jirgi (mai dauke da mutane) daya rafa sauka a kan doron wata, Daya daga cikin Yan-sama jannati da ake kira da suna Michael Collins, shine ya zauna a cikin Jirgi, yayin da Neil Armstrong da Buzz Aldrin suka sauka suka yi tafiya akan doron wata.

Jirgin Apollo mai lamba 13 kuwa, shi bai sauka akan doron wata ba saboda wata matsala daya samu, abinda su matukan jirgin suka yi shine, shawagi a kewayen Duniyar Wata Sannan suka dawo zuwa wannan Duniya tamu.

Binciken da muka yi ya dada tabbatar mana da cewa, akwai shirye-shirye da dama da aka sha yi, game da abin da ya shafi sararin samaniya, tun daga lokacin da aka harba Jirgin Sputnik a 1957 zuwa Jirgin da aka harba Duniyar Mars a 1999 wanda bai ci nasara ba.Hakan ya nuna cewa akwai wadansu kasashe a Duniya da suke da shiri game da sararin samaniya, to Amma kasar Amurka ce kadai Kasar da ta tura Yan-sama Jannati zuwa Duniyar wata.

To sai dai akwai kasashen da suke da sha’awar kaddamar da shirin bude tashar bincike na sararin samaniya, inda a yanzu haka, akwai kasashe 16 wadanda suka dukufa ka’in-da-na’in wajen gina tashoshin binciken sararin samaniya na kasa-da-kasa.Kuma bincike ya tabbatar da cewa, kasar Sin wato Chaina, tana nan tana bunkasa shirinta na sararin samaniya, inda take da aniyar harba Jirgin kumbo mai dauke da Yan-sama Jannati zuwa Duniyar wata. Saboda haka nan da shekaru 10 zuwa 20 masu zuwa, idan Malam mu’azu ya sake aiko mana da wannan Tambaya zai iya samun amsar da ta sha ban-ban da wadda muka bashi a halin yanzu.