1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sanda sun awon gaba da jagoran ´yan adawa a Zimbabwe

January 23, 2008
https://p.dw.com/p/CwIr

A ƙasar Zimbabwe an kame shugaban ´yan adawa na ƙasar Morgan Tsivangirai kamar yadda lauyansa ya nunar. A cikin daren jiya ´yan sanda suka yi awon gaba da jagoran na ´yan adawa. A yau laraba jam´iyarsa ta Movement for Democratic Change ta shirya gudanar da zanga-zangar, domin ƙara matsawa shugaba Robert Mugabe lamba da a sake fasalin kundin tsarin mulkin ƙasar wanda zai tabbatar da kamanta adalci a zaɓen shugaban kasa da na ´yan majaliar dokoki da za a yi cikin watan Maris. ´Yan sanda sun haramta zanga-zangar saboda gudun yin artabu.