1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240608 Nahost Dschenin Polizei

Aßmann, Tim / Dschenin (BR)June 24, 2008

Taron birnin Berlin na mayar hankali kan inganta rundunar ´yan sandan Flasɗinu

https://p.dw.com/p/EPrk
Merkel da sauran mahalarta taron Falasdinu a BerlinHoto: AP

An buɗe wani babban taro na yini guda a birnin Berlin domin duba hanyoyin taimakawa Yankunan Falasɗinawa musamman a fannonin tsaro da shari´a. Ƙarin bayani dangane da aikin jami´an ´yan sandan Falasɗinu a garin Jenin na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Adnan Qalawleh shi ne shugaban rundunar ´yan sandan sintiri a garin na Jenin dake Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. A cikin wata motar sintiri da gwamnatin tarayyar Jamus ta bawa hukumar Falasɗinu kyauta, Adnan Qalawleh ya ratsa ta wani rawul inda ´yan sanda ke binciken motoci.

Qalawleh: Ya ce "Yana da muhimmanci a riƙa tabbatar da bin doka da oda. A nan dai masu sayayya na da yawa shi yasa bai kamata a samu cunƙoson motoci ba. Ya kamata mutane su rika girmama juna. ´Yar ƙaramar gudunmawar da muke bayar kenan. Hakan kuwa na yin tasiri a tsakanin jama´a."

Ban da ´yan sandan masu ba da hannu akwai kuma wasu ´yan sanda na wata runduna ta musamman masu rataye bindigogin Kalashnikov a kafaɗa waɗanda aikinsu shi ne tabbatar da tsaro. To sai dai Adnan Qalawleh ya ce mutanensa ba sa iya taɓuka komai idan sojojin Isra´ila suka kai samame a garin na Jenin.

Qalawleh: Ya ce "Wani lokacin Isra´ila na sanar da mu cewa za ta shigo cikin garin, amma a lokuta da dama tana yi mana dirar mikiya ne. Wannan na ci mana tuwo a ƙwarya saboda haka ya kamata a yi wani abu."

Shi kuwa Fariss Suleiman mai kantin sayar da wayoyin salula a tsakiyar garin tuni yayi da lokacin da babu tsaro kwata-kwata a garin. Amma yanzu abubuwa sun canza inda ake ƙara amincewa da ´yan sandan.

Suleiman: Ya ce "Aikin ´yan sandan ya ingantu musamman wajen yaƙi ´yan fashin motoci. A da doka a rubuce ta ke amma yanzu ana aiwatar da ita."

A ofishinsa dake a hedkwatar ´yan sanda ta garin Jenin Mahmoud Abu Al-Rub mai shekaru 37, wanda a da ya ke Gaza, bayan ƙarin horo da ya samu a wata kwalejin ´yan sanda ta ƙasar Indiya yanzu shi ne muƙaddashin shugaban rundunar ´yan sanda a Jenin.

Al-Rub ya ce "Yanzu mun samu ƙarin ilimi ko dai a manyan makarantu ko a jami´o´i. Wasunmu sun koma fannin shari´a wanda haka yake sauƙaƙa aikinmu da kotuna. Duk da matsaloli nan da can da muke samu, muna gudanar da aikinmu yadda ya kamata."

Jami´in´yan sanda ya ce aikin horaswar wanda ƙasashen Turai da Amirka ke ɗaukar nauyinsa yana samun nasara. To sai dai duk da haka da sauran rina a kaba, domin suna buƙatar kayan aiki na zamani musamman a fannin yaƙi da masu aikata manyan laifuka. Wani muhimmin abu kuma shi ne Isra´ila ta daina yin katsalanda a cikin aikin jami´an tsaron na Falasɗinu.