1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Kenya sun tarwatsa zanga-zangar 'yan adawa

Mohammad Nasiru AwalApril 25, 2016

'Yan adawa na zargin gwamnatin Kenya da juya akalar hukumar zaben kasar kuma sun yi kira da a rusa hukumar.

https://p.dw.com/p/1IcST
Kenia Unruhe Polizei Konfrontation
Hoto: picture alliance/dpa/D. Irungu

'Yan sandan kasar Kenya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa magoya bayan 'yan adawa da jagororinsu da ke wata zanga-zanga a wajen ofishin hukumar zaben kasar. Jagororin 'yan adawa na saka ayar tambaya game da ko hukumar mai zaman kanta tana da cikakken 'yancin gudanar da aikinta. Sun nuna bukatar rusa hukumar zaben gabanin manyan zabukan da za a yi a kasar a shekarar 2017. Bonny Khalwale sanata ne na jam'iyyar adawa ya zargi gwamnati da juya akalar hukumar zaben.

Ya ce: "Mun zo ne mu gana da hukumar zabe mai zaman kanta, ba mun zo ne don mu gana da 'yan sanda ko gwamnati ba. Me ya sa gwamnati ke jan akalar hukumar. Me ya sa suke harbin mu da hayaki mai sa kwalla? Me ya sa suke harbi a kanmu? Ba mun zo ne don mu kifar da gwamnati ba. Mun zo mu nuna fushinmu ga hukumar zaben da ba ta aikinta daidai."