1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

’Yan ta kifen Ƙungiyar Hamas, sun yi barazanar kai hare-hare cikin Isra’ila.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burk

A wata sabuwa kuma, rukunin ’yan ta kife na kungiyar Hamas, ya mai da martani ga Isra’ilan da yin barazanar kai wa ƙasar bani Yahudun sabbin hare-hare a cikin harabobinta. Ƙungiyar ta kuma yi Alllah wadai da nuna ƙarfin sojin da Isra’ilan ke yi wa Falasɗinawa a zirin Gaza.

A halin yanzu dai, ƙungiyoyi uku da ke ikirarin yin garkuwa da sojan Isra’ilan, sun ce suna bukatar a sako fursunonin Falasɗinawa dubu ne da Isra’ilan ta ɗaure a gidajen yarinta. Amma Firamiya Ehud Olmert ya lashi takobin cewa, gwamnatinsa ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Isar’ilan da Falasɗinawa ya ɓarke ne, bayan da mayaƙan ƙungiyoyin Falasɗinawan suka kame wani cofur na sojin Isra’ilan, Gilad Shalit, mai shekaru 19 da haihuwa, a ran 25 ga watan jiya, a wani harin da suka kai wa rukuninsa a kan iyakar zirin Gaza da ƙasar bani Yahudun.