1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe sojin Nijar biyar

November 8, 2016

Sojojin Nijar biyar sun mutu wasu uku sun jikkata a lokacin wani harin ta'addanci da aka kai kansu a wannan Talata a kauyen Banibangou na cikin kasar Ouallam kan iyaka da kasar Mali

https://p.dw.com/p/2SLEN
Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewaR sojojin gwamnatin kasar biyar sun halaka a yayin da wasu uku suka jikkata a lokacin wani harin ta'addanci da wasu suka kai tun da sanhin safiyar wannan Talata a kauye Banibangou na cikin kasar Ouallam na Kudancin kasar kusa da kan iyaka da kasar Mali.Wani babban jami'in sojan kasar ta Nijar wanda bai so a bayyana sunansa ba ya kwarmata wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wasu sojojin hudu sun bata biyo bayan kaddamar da harin wanda ya ce an kai shi ne da misalin karfe hudu na daren Litanin washe garin wannan Talata. Karimu Bureima Dan majalisar dokoki daga garin na Banibangou ya tabbatar wa da wakiliyar DW Ramatou Issa Wanke karin bayani kan wannan hari.

A watan Oktoban da ya gabata ma dai sojojin gwamnatin kasar ta Nijar 22 suka halLaka a cikin wani harin ta'addanci da wasu maharan suka kai kan bataliyar sojojin Nijar da ke a sansanin 'yan gudun hijira na Tazelit cikin jihar Tawa.