1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan taliban sun yi belin pirsinoni 8 na Korea ta Kudu

August 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuCp

Dakarun taliban a ƙasar Afghanistan,sun yi belin pirsinoni 8, daga jimilar mutane 19, yan ƙasar Korea ta Kudu ,da su ka yi garkuwa da su tun ranar 18 ga watan Juli da ya wuce.

Da farkon sahiyar yau, sun yi belin pirsinoni 3 dukkan su mata, sai kuma jim kaɗan su ka ƙara sallamar pirsinoni 5 wanda su ka haɗa da mata 4 da namiji ɗaya.

Hukumar bada agaji ta ƙasa da ƙasa, wato Red Cross ta karbi mutanen 8.

A cewar kakakin wannan hukuma,tsafin pirsinonin na cikin ƙoshin lahia, saidai akwai matuƙar gajiya da kasala tare da su.

A jiya ne aka cimma yarjejeniyar belin mutanen 19 a sakamakon tantanawa mai tsauri da ta haɗa wakilan gwamnatin Korea ta kudu, da yan talibanTaliban.

A wannan tananawa, hukumomin Seoul, sun amince su janye sojojin su 200, da ke aiki a cikin rundunar ƙasa da ƙasa a Afghanistan.

Yan taliban, su yi alƙawarin sallamar koreyawan 19, nan da kwanaki 3 zuwa 4, muddun su ka cimma wannan buri.