1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawaye sun fafata da dakarun Chadi

November 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuaS

Dakarun gwamnati a kasar Chadi sun fafata da yan tawaye a kusa da garin Abeche dake gabashin kasar.

Maaikatan agajai a Abeche sunce sunji karar harbin bindigogi a wajen birnin.

Yan tawaye dai sun kara kaimin hare hare da suke kaiwa cikin yan watannin nan a kokarinsu na hambarar da gwamnatin Idriss Deby.

Gwamnatin dai ta zargi kasar Sudan da laifin baiwa yan tawayen taimako,wanda kuma tuni Sudan din ta karyata.

A jiya jumaa ne kuma gwamnatin Chadi ta kara waadin watannin 6 kann dokar ta bacin da ta kafa a ranar 13 ga watan nuwamba a N’djamena da wasu yankuna ciki har da gabashin kasar.