1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YAN TAWAYE SUNYI WATSI DA WAADIN AJIYE MAKAMAI

November 17, 2003

ZAINAB AM ABUBAKAR

https://p.dw.com/p/Bvna
Bayan Shugabannin kasashen Afrika sun cimma rattaba hannu kann yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin yan tawayen kasar Burundi da gwamnatin wannan kasa a wani taro da suka gudanar a jiya a kasar Tanzania,tare da bawa yan tawayen FNL waadin watannin uku na ajiye makamai domin kawo karshen yankin basasan wannan kasa,ayau kungiyar tayi fatali da wannan waadi da aka bata. Shugabannin kasashen da suka halarci wannan taro na Birnin Darussalam jiya sunyi fatan cewa wannan yarjejeniya da aka cimma zai kawo karshen dukkan rikice rikice da aka fuskanta tundaga shekara ta 2000,tare da kawo karshen fadan daya haddasa asaran rayukan mutane sama da dubu dari uku a shekaru 10 da suka gabata a wannan kasa dake tsakiyar gabashin Afrika. To sai dai kakakin kungiyar yan tawayen na FNL ,karama daga cikin kungiyoyin yan tawayen Burundin,wadanda kuma suka kunshi yan kabilar Hutu,yace basu amince da wannan waadi da shugabannin na Afrika suka basu tare da wasu wakilan kabilar ta Hutu a taron nasu na jiya.

Mai magana da yawun kungiyar Pasteur Habimana yace kungiyarsa zata tattauna kawai da yan kabilar Tutsi wadanda sune ke rike da harkokin tsaro na kasar amma ba shugaban Domitien Ndayizeye,wanda yake dan kabilar Hutu ne ba.Ya fadawa manema labaru ta wayan tangaraho cewa yan kabilar ta tutsi ne sukayi musu kisan gilla,domin haka dasu ne zasu tattauna batun sasantawa amma ba da dan uwansu Hutu ba.

Yan Tutsin dai wadanda har yanzu sune ke rike da harkokin tsaro a kasar ta Burundi,sune kashi 15 daga cikin dari na yawan jamaar wannan kasa.

A jiya ne shugaba Domitien ya rattaba hannu tare da shugabannin kungiyar yan tawaye mafi girma a ta FDD kuma ta yan kabilar hutu,a birnin Darussalan bukin daya samu halartan shugabannin kasashen Afrika.A wannan taron ne aka bawa yan FNL din wannan waadi na ajiye makaman fada cikin watanni uku,tare da cimma daidaituwa dasu ko kuma su dandana kudarsu. A dangane da hakane kakakin yan tawayen ana FNL yace babu yadda zaa magance matsalar Burundi a Darussalam,tunda matsalar a Burundi take dole anan zaa maganta ta amma ba a wata kasa ba. Burundi kasa ce dake fuskantar matsaloli na fadan kabilanci tun data samu yancin kai a shekara ta 1962 daga kasar Belgium.Kimanin mutane dubu 300 suka rasa rayukansu a wannan fada,wanda ya fara da kisan gilla da akayiwa shugaban hutu na farko a shekara ta 1993 Ndadaye,wanda kuma sojojin kasar yan kabilar Tutsi suka aikata. Yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba hannu akai dai na nufin kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar da yan tawayen FDD ,tare da shigar da yan tawayen cikin harkokin tsaron Brundi wanda ahalin yanzu yake hannun yan Tutsi kadai.