1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen Abzunawa sun sako sojin gwamnati

September 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuBC

Yan tawayen Abzunawa na ƙungiyar MNJ a jamhuriyar Niger sun sanar da sakin sojojin gwamnati su goma sha huɗu bayan da Libya ta sanya baki. Wata majiya ta yan tawayen ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ta saki sojojin ne bisa roƙon da shugaban ƙasar Libya Moamer Gaddafi ya yi musu. A ranar 7 ga wannan watan ne ƙungiyar ta baiyana kama sojojin gwamnati su shidda yayin da suka kai farmaki a wani barikin sojin dake arewacin Niger. Tun da farko yan tawayen na riƙe da sojoji 33 waɗanda suka kama tun a cikin watan Yuni. A watan da ya gabata shugaban ƙasar Niger Tanja Mamadou ya nemi haɗin kan mahukunta a birnin Tripoli domin tabbatar da zaman lafiya a cikin ƙasar. Tun dai a cikin watan Fabrairu na wannan shekarar ake ta artabu tsakanin sojojin gwamnatin ta Niger da ƙungiyar yan tawayen Abzunawan ta MNJ.