1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen Darfur da sabuwar gwamnatin Sudan

Zainab A MohammadSeptember 23, 2005

Yan tawaye sunyi watsi da sabuwar gwamnatin hadin kan kasa

https://p.dw.com/p/BvZS
Hoto: AP

Kungiyar yan tawaye data cafke wani gari dake lardin Darfur dake yammacin Sudan a yan kwanakin nan,tayi Allah wadan gwamnatin hadin kan kasa dad a aka kafa a wannan makon a wannan kasa,a dangane da hakane tace yaki kadai ne zai tabbatar da gwamnatin adalci a sudan.

Sanarwar da kungiyar yan tawaye ta SLA ta fitar ta hannun Mahjoud Hussein,na bayanin cewa sabuwar gwamnatin hadin kan kasar tayi watsi da mafi yawan alummomin Sudan,tare da nuna wariya wa sassa da tun a baya akayi watsi dasu cikin harkokin gwamnati.

Sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan janairu ne dai ,aka kafa wanna gwamnatin hadin kan kasa a sudan din,batu da ake ganin ya kawo karshen yakin basasa daya dauki sama da shekaru 20 yana gudana tsakanin yan tayaen kudancin kasar da gwamnatin Khartum.

Wasu mazauna kudancin kasar dai sun bayyana rashin gamsuwarsu da sabuwar majalisar gudanarwan.Adangane da hakane suke ganin cewa babu yadda zaa kafa ingantacciyar gwamnatin hadin kan kasa ba tare da an fito filin daga ba.

A ranar talata nedai kungiyar ta SLA ta sanar dacewa ta cafke garin Sheiria,wanda keda yan gudun hijira kimanin dubu 33,fafatawar data ritsa da rayukan dakarun sojin gwamnatin Sudan kimanin 80.

Wannan sabon rikici dai ya barke ne adaidai lokacin da wani bangare na kungiyar yan tawayen Darfur din dake kiran kanta justice and equality movement ,JEM a takaice ke gudanar da taron sulhu da bangaren gawamnati a Abujan tarayyar Nigeria.

Tun a shekarata 2003 kungiyoyin yan tawayen biyu suka kaddamar da hare hare wa rundunar gwamnatin da aka rusa ,adangane da kokensu nacewa ,ana nuna musu wariya cikin lamuran gudanar da kasa.Fadace fadace dai sun dan lafa a lardin na Darfur a shekarar data gabata,amma watan daya gabata am fara fafatawa tsakanin bangarorin yan tawayen dana gwamanati.

A dangane da hakane sakatare general na MDd Kofi Annan yayi kira ga gwamnatin Sudan da abokan adawanta dake tattauna yiwuwan sulhu a Nigeria,dasu gaggauta cimma matsaya guda,domin kawo karshen wahalhalu da mazauna lardin darfur ke cigaba da kasancewa ciki.

A wata sanarwa daya aike ,jagoran Mdd ya bukaci mahalarta taron na Abuja ,dasudauki dukkan matakan da suka dacewa na ganin cewa sun kawo karshen halin kuncin rayuwa da Darfur ke ciki a halin yanzu,a wannan zagayen tattaunawan.

Tun ranar 15 ga wannan wata nedai aka bude sabon taron tattaunawa tsakanin kungiyoyin yan tawaye biyu dake lardin Darfur a yammacin Sudan,da bangaren gwamnati akarkashin jagorancin kungiyar gamayyar Afrika Au,a Abujan tarayyar Nigeria.Gwamnatin Sudan din dai tayi has ashen cimma yarjejeniya daga yanzu zuwa karshen wannan shekara.

Duk dacewa kungiyoyin yan taywaen darfur din biyu ke halartan taron,bangare guda na SLM ce kadai keda wakilci a Abujan,ayayindfa gudan ke cigaba da fafatawa da dakarun gwamnati a yammacin Sudan din.

Ire iren wadannan tattaunawa a baya dai sun gaza cimma tudun dafawa,saboda zargin da bangarorin kewa junansu na keta dokar tsagaita wuta.