1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

’Yan tawayen Darfur na tilasa wa ’yan gudun hijira ɗaukan makamai.

May 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buy2

Duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ƙulla tsakanin gwamnatin Sudan da ’yan tawayen yankin Darfur, rahotanni na nuna cewa har ila yau, ’yan tawayen na ci gaba da tilasa wa ’yan gudun hijira, musamman yara daukan makamai. A galibi hakan na aukuwa ne a sansanonin ’yan gudun hijiran da ke ƙasar Cadi, inda aka tsugunad da kusan mutane dubu ɗari 2 da suka ƙaurace wa matsugunansu a yankin na Darfur, inji kakakin Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya, Ron Redmond.

Da yake yi wa maneman labarai jawabi a birnin New York, kakakin ya ƙarfafa cewa, ba daidai ba ne, a yi amfani da sansanonin ’yan gudun hijiran wajen tilasa wa yara masu shekaru ƙasa da 18, shiga aikin soji.

A cikin watan Maris na wannan shekarar, kusan mazaje da yara dubu 4 da ɗari 7 daga sansanonin Breidjing da Treguine ne ’yan tawayen suka tilasa musu shiga aikin soji.

Kakakin dai ya bayyana cewa, Hukumar ta yi shawarwari da jami’an gwamnatin Cadi a cikin watanni biyun da suka wuce, inda ta nanata musu irin nauyin da ya rataya a wuyar gwamnatin ƙasar dangane da kare lafiyar ’yan gudunn hijiran, kamar yadda yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta ajiye.