1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen Darfur sun cimma matsaya ɗaya

August 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuES

Sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai Havier Solana ya maida martani ga matakin da ƙungiyoyin tawayen Darfur su ka cimma, a taron da su ka kammalla jiya, a birnin Arusha na ƙasar Tanzania.

Idan dai ba a manta ba, ƙungiyoyin tawaye 8 na yankin Darfur bisa jagorancin ƙungiyar taraya Afrika da Majalisar Ɗinkin Dunia sun shiraya zamna taro inda su ka matsaya matsaya ɗaya a game da daftarin buƙatoci na haɗin gwiwa, wanda za su gabatarwa gwamnatin ƙasar Sudan.

Ƙungiyar taraya turai ,ta yi lale marhabin da wannan matsayi, wanda a cewar ta, matakin ne ƙwaƙƙwara na kawo ƙarshen rikicin yankin.

Eu ta alƙawarta ci gabada bada gudummuwa, a yunƙurin warware wannan rikici, sannan ta yi kira ga gwamnatin Khartum da yan tawaye, su bada haɗin kai ga ayyukan rundunar ƙasa da ƙasa,wad da Majalisar Ɗinkin Dunia, tare da ƙungiyar Taraya Afrika za su tura a Darfur.