1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan tawayen FARC a Kolumbia sun saki wasu mata biyu da suka yi garkuwa da su

January 11, 2008
https://p.dw.com/p/Co3Z

Matan nan biyu da aka sako su bayan an shafe shekaru masu yawa ´yan tawayen ƙungiyar FARC a ƙasar Kolumbia suna garkuwa da su, sun isa Venezuela. A birnin Caracas, shugaban Venezuela Hugo Chavez ya tarbi matan biyu da suka haɗa da tsohuwar ´yar majalisar dokoki Consuleo Gonzales da kuma Clara Rojas tsohuwar mai yiwa ´yar takarar shugaban ƙasar Kolumbia Ingrid Betancourt yakin neman zabe. Shugaban Chavez ya shiga tsakani aka saki matan. A cikin watan fabrairun shekara ta 2005´yan yaƙin sunkurun FARC suka sace Rojas da Betancourt. A cikin hirar da aka yi da ita Rojas ta ce shekararta uku rabonta da ganin Betancourt.