1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen FUCD a Tchad,sunyi barazanar sabbin hare hare

Zainab A MohammadApril 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6l

Shugabannin babbar kungiyar yan tawaye na kasar Tchadi sun gabatar da wata sanarwa dake gargadin cewa ,dakarunsu zasu kaddamarda sabbin hare hare ,gabannin zaben shugaban kasa na ranar 3 ga watan gobe,tare da yabawa Amurka wadda ta bukaci da ajinkirta wannan zabe.Wakilan kungiyar adawa ta FUCD,dake da matsugunnensu a kasar faransa, sunyi ikirarin cewa kungiyarsu nada kimanin kashi 80 daga cikin 100 na alummar tchadi,amatsayin magoya baya,kuma suna isassun mutane da makamai da zasu hambare shugaba Idriss Deby daga kujerar mulkinsa.Hare haren yan tawaye a kasar Tchadin ranar 13 ga wannan wata dai,yabar mutane 350 mace,rikicin daya haifar da shakku dangane da harkoki na tsaro a wannan kasa dake tsakiyar Afrika,amma cikin gaggawa shugaba Deby ya karyata.To sai dai a taron manema labaru daya gudanar yau a birnin Paris,directan harkokin waje na kungiyar yan tawaye mafi girma Raoul Laona gong yace,a shirye suke suyi amfani da karfin soji kafin ko kuma bayan zaben na 3 ga wata,inda yace ko shakka babu zaa tabka magudi,don haka bazasu shiga ba.