1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen Ivory Coast sunyi watsi da sunayen Premier

Zainab A MohammadNovember 18, 2005
https://p.dw.com/p/Bu7n

ABIDJAM

Yan tawayen kasar Ivory Coast sunyi watsi da jerin sunayen mutanen aka zaba domin mukamin prime ministan kasar,wanda masu shiga tsakani dake kokarin gano bakin zaren warware rikicin wannan kasa suka zaba,saboda babu sunan shugabansu a jerin sunasyen.

Tun a yunkurin kifar da gwamnatin Gbagbo daya ci tura a shearu 3 da suka gabata nedai,I)vory Coast ta dare biyu tsakanin arewaci dake hannun yan tawaye,da kuma kudanci dake karkashin gwamnati.

A karkashin tsarin mdd na warware takaddaman siyasa a wannan kasa dai,zaa nada sabon prime minista.

A makonni biyu da suka gabata nedai shugaban Nigeria kuma na kungiyar gamayyar Afrika AU,Olushegun Obasanjo ya gana da bangaren gwamnati dana yan tawayen kasar a Ivory Coast akan sabon prime ministan,tare dayi musu alkawarin gabatar sunayen wadanda zasu cancanci wannan mukami.

A jiya nedai MInistan harkokin waje na Nigeria Oluyemi Adeniji,ya gana da shugaban yan tawayen Guillaume Soro,a garin Bouake ,inda ya gabatar masa da sunayen mutane hudu domin mukamin premiern Ivory coast.Wadannan mutane hudu dai sune aka tantance daga cikin jerin sunaye 16 da aka gabatar tun da farko.