1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

’Yan tawayen Sri Lanka na zargin dakarun gwamnati da kai musu hare-haren bamabamai.

November 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bub2

Ƙungiyar nan ta Tamil Tigers, ta ’yan tawayen da ke gwagwarmaya da dakarun gwamnati a ƙasar Sri Lanka, ta ce jiragen saman yaƙin dakarun gwamnati sun kai wa gurabanta hare-haren bamabamai a yankin Kilinochi da ke arewacin ƙasar. Wani kakakin ƙungiyar ya faɗa wa kamfanin dilllancin labaran Reuters cewa, kusan bamabamai 20 ne jiragen suka jefa musu. Amma a ɓangaren rundunar sojin ƙasar kuma, kakakinsu Birgediya Prasad Samarasinghe, ya ce ba shi da wata masaniya game da harin mayaƙan sama.

Fafatawar da ɓangarorin biyu suka yi ta yi da juna a wannan shekarar ta janyo asarar rayukan fararen hula fiye da dubu 3 a ƙasar. A halin yanzu dai mafi yawan ’yan ƙasar na fargabar cewa al’amura za su ci gaba da taɓarɓarewa har a koma yaƙin basasa, irin wanda ya ɓarke a cikin shekarar 1983, inda aka ƙiyasci cewa kusan mutane dubu 67 ne suka rasa rayukansu.