1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen Uganda sun kai sabon hari

January 9, 2006
https://p.dw.com/p/BvD5

Mutane a kalla uku ne suka rasa rayukan su, wasu kuma 12 suka jikkata , bayan da yan kungiyyar tawaye ta LRA a Uganda suka kai wani hari a arewacin kasar.

Bayanai dai sun nunar da cewa yan tawayen sun bude wuta kann mai uwa da wabi ne a cikin cincirin don masu raye raye da wake wake a arewacin kasar ta Uganda a karshen makon nan daya gabata.

A cewar kakakin sojin kasar ta Uganda, wato Chris Magezi, jami´an su sun samu galabar bin sahun yan tawayen inda suka samu damar kashe mutum biyu daga cikin su.

Bugu da kari, kakakin sojin ya kuma tabbatar da cewa a wata arangama data wanzu a tsakanin su da yan tawayen a gulu, sun kuma kashe mutum biyar daga cikin yan kungiyyar ta LRA.