1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin musulmi a nan Jamus.

December 28, 2005

Tun da aka yi garkuwa da bajamushiyar nan Susanne Osthoff a kasar Iraqi ne, wata muhawara mai tsanani ta barke a nan Jamus game da irin rawar da musulmin wannan kasar ke takawa, wajen goyon baya ko kuma nuna kyama ga manufar ta'addanci, wadda ake aiwatarwa da sunan addinin islama.

https://p.dw.com/p/BvU5
Nadeem Elyas
Nadeem ElyasHoto: dpa

A nan Jamus dai akwai musulmi da yawa, wadanda suka hada da `yan kasa wato Jamusawa da kuma baki mazauna nan kasar da iyalansu. Sau da yawa dai, a kan sami hauhawar tsamari tsakanin musulmin da wadanda ba musulmi ba. Su dai musulmin na sukar kafofin yada labarai ne da rikitda da jama’a game da addinin islaman, ta irin bayanan da suke bugawa game da addinin. Ko yaushe aka yi wata tarzoma ko tashe-tashen hankulla, sai ka ga kafofin yada labarai sun jibinta su da addinin na islama.

Don yi wannan halin da ake ciki gyara da kuma bayyana wa al’umman wannan kasar inda addinin islaman ya nufa takamaimai kuma ya mai da alkibla ne, kungiyoyin musulmi daban-daban na nan Jamus, suka kafa wata kungiya ta uwa-uban duk sauran kungiyoyin, wadda aka yi wa sunan Majalisar koli ta Musulmin Jamus. Ita dai wannan kungiyar, ita ce ta zamo kamar kakakin duk wani musulmi na nan kasar. A ko yaushe, ita ce ke ba da bayanai kan matsayin musulmin Jamus game da al’amura daban-daban da ke wakana a duniya baki daya.

A lal misali a kwanakin baya da suka wuce, an yi ta yada labarin wata bajamushiya da aka yi garkuwa da ita a Iraqi. To kai tsaye ne dai shugaban Majalisar kolin ta Musulmin Jamus, Nadeem Elyas, ya kira wani taron maneman labarai, inda ya yi Allah wadai da garkuwar da aka yi da bajamushiyar da direbanta, ya kuma bayyana cewa, addinin islama ko kadan ba ya goyon bayan irin wannan danyen aikin. Daga baya ma, sai da shugaban Majalisar musulmin ya ce a shirye yake ya ba da kansa ga masu garkuwa da bajamushiyar, don su sako ta, shi ya ci gaba da maye gurbinta a hannunsu, har zuwa lokacin da suka cim ma burinsu, ko kuma suka yanke shawara kan makomarsa a hannunsu.

Wannan matakin da kungiyar ta dauka dai, ya sanya wata alama a nan Jamus, wadda bisa kanta ne ma kafofin yada labarai da dama ke kokarin gano yadda dangantaka take a halin yanzu, tsakanin musulmi da wadanda ba musulmin ba a nan Jamus. Game da hakan ne dai gidan rediyon Deutschlandfunk ya yi wata doguwar fira da Nadeem Elyas, shugaban Majalisar kolin ta Musulmin Jamus, inda aka yi masa tambayoyi da dama a kan batutuwan da suka shafi zaman cude ni in cude ka, tsakanin al’ummai daban-daban da ke zaune a nan kasar.

Ko yaya Jamusawa suka mai da martani ga matakin da ya dauka na sadaukad da kansa, don cim ma sako bajamushiyar nan Susanne Osthoff da aka yi garkuwa da ita a Iraqi ?

Game da wannan tambayar dai, Nadeem Elyas ya bayyana cewa:-

„Gaba daya dai, jama’a sun bayyana gamsuwarsu da matsayin da muka dauka; da muslmi da wadanda ba musulmi ba, duk sun yi ta aiko mana sakwanni na nuna goyon bayansu ga matsayinmu, ta hanyar wayar tarho, da e-mail da wasiku. Kafofin yada labarai ma, sun buga kyawawan rahotanni a kan wannan batun. Hakan kuma, na nuna cewa, matsayin namu, matsayi ne na kirki, kuma mai ma’ana.“

Game da tambayar cewa, ko wannan matsayin ya janyo wani sassaucin tsamari a yanayin da musulmi da wadanda ba musulmin ba ke ciki a nan Jamus, Nadeem Elyas ya bayyana cewa:-

I, to yanzu dai, an fahimci cewa da gaske muke. Da can kuwa, ana kallonmu ne da idanun shakku, duk da cewa a ko wane lokacin da aka kai harin kunan bakin wake da sunan addinin islama, ko a duniyar musulmi ne ko kuma a ketare, mu kan bayyana matsayinmu game da wannan danyen aikin, muna kuma masu nisantad da kanmu daga irin wannan aika-aikan. A lokuta da dama dai akwai masu sukarmu da cewa, muslmi suna goyon bayan irin wadannan ayyukan na ta’addanci. Suna furace-furace ne na baka kawai. Amma a zuci, goyon bayan `yan tarzoma suke yi.

Yanzu kam, an lura da cewa da gaske muke. Mun dai sha nanata cewa, bam u da wata jibinta da wadannan ayyukan ta’addancin, ba ma nuna musu zumunci, kuma muna duk iyakacin koakarinmu wajen nuna adawa gare su.“