1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240508 Katholikentag Religionsfreiheit

Kolakowski, Peter / Osnabrück (DW Deutsch) May 29, 2008

Muhawwara kan ´yancin yin addini a Turai da kuma ƙasashen duniyar musulmi.

https://p.dw.com/p/E8Gg
Ministan tsaro Schäuble da wakilin musulmin Jamus AlbogaHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka. Barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da yin nazari kan batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi daban daban a wannan duniya ta mu.


Ƙudurin kare haƙƙin ɗan Adam na shekara ta 1950 ya bawa kowa tabbacin tafiyar da addini ba da wata tsangwama ba musamman a nan nahiyar Turai. Hatta a nan Jamus kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin cikakken ´yancin tafiyar da addini. To yaya ´yancin tafiyar da addini ya ke a wasu ƙasashe musamman a ƙasashen musulmi? Shin ko Kiristoci a waɗannan ƙasashe suna iya tafiyar da addininsu ba da wani tarnaƙi ba? Shin ko su ma musulmi a nan Turai suna samun cikakkiyar kariyar yin addininsu ko kuma a´a suna fuskantar wariya? Akan wannan batu wakilan ƙungiyoyin musulmi da na majami´un Katholika suka tattauna a wani zauren musayar ra´ayoyi game da ´yancin tafiyar da addini a Turai da kuma duniyar musulmi.


Bayanan da Dr. Otmahr Oehring na sashen ´yan mishan na majami´ar Katholika ya yi game da ´yancin tafiyar da addini a ƙasashen musulmi, abin damuwa ne. To amma ya ce akwai banbamci daga wata ƙasa zuwa wata dangane da wariyar da ake nunawa Kiristoci. Ya ce yayin da mabiya addini Kirista a ƙasashe kamar Jordan da Syria suke da ´yancin tafiyar da addininsu ba da wata tsangwama ba. To amma duk da haka ba za a iya cwea suna da cikakken ´yancin yin addini ba musamman wajen samun izinin gina coci ko wuraren ibada. Dr. Oerhing ya ƙara da cewa.


1: "A wani ɓangaren akwai matsaloli dake da alamun an magance su. Amma da akwai tarin wasu matsalolin waɗanda kamar a lokutan baya ma har yanzu babu wata alama da ke nuni da za a warware su nan gaba kaɗan. Saboda haka ya zama wajibi a ci-gaba da tattaunawa da wakilan musulmi da ƙasashen duniyar musulmi domin a samu mafita. Wani muhimmin batu a dangane da ´yancin yin addini ko kuma yake da dangantaka da ´yancin yin addinin shi ne damar canza addini. In ban da ƙasar Turkiya babu wata ƙasa ta musulmi da ta yarda da canza addini."


Wannan matsalar dai ta fi tsanani ne a ƙasashe kamar su Iran, Pakistan da kuma Afghanistan. A waɗannan ƙasashen yin ridda a fili ko canza addini daga musulunci zuwa kirista daidai ya ke da wani hukuncin kisa. Hatta ma a ƙasar Turkiya wadda ke ƙoƙarin shiga cikin ƙungiyar tarayyar Turai kuma ta sanya hannu kan ƙudurin kare haƙin ɗan Adam na Turai, ba a cikakken ´yancin yin addini, inji Dr. Oehring wanda ya taɓa zama a ƙasar ta Turkiya har tsawon shekaru 18.


2. "Kuskure ne yadda kafofin yaɗa labaru ke siffanta Turkiya a matsayin wata ƙasa da babu ruwanta da addini. Ko kaɗan ba ƙasa ce mai maraba da kowane addini ba, duk da cewa tana kwatanta kanta a matsayin ƙasar da ke nesanta kanta da bin dokokin addini. An sha jan kunnen Turkiya musamman a dangane da ´yancin yin addini da rashin girmama matsayin tsiraru waɗanda ba musulmi ba."


Halin da su ma musulmi suke ciki a ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai ciki har da tarayyar Jamus ya bambanta da iƙirarin da waɗannan ƙasashe ke yi cewa akwai walwala da ´yancin yin addini ba da tsangwama ba a cikinsu. Masanin kimiyyar addinin musulunci Bekir Alboga ya yi ƙorafi game da wariyar da hukumi ke nunawa addinin musulunci a Jamus. Alboga wakilin ƙungiyar musulmi Turkawa mai kula da addini a tattaunawar fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da ala´adu a Jamus ya ce a kullum ji suke tamkar ba za a taɓa amincewa da su a matsayin wata gamaiyar addini ba. Ya ce har yanzu babu wani ƙwaƙwaran shiri daga ɓangaren ´yan siyasa na bawa addinin musulunci matsayi daidai da majami´un kirista.


3. "Ko da yake a ɓangare ɗaya ana ƙoƙarin kyautatawa tare da warware matsalolin zamantakewa da musulmi, amma a ɗaya ɓangaren har yanzu ana nuna son kai. Tun bayan 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 ake yiwa addinin muslunci kallon wani sabon abokin gaba a Jamus."


Alboga yayi suka da kakkausar harshe dangane da kalaman da shugaban majami´ar Evangelika a Jamus, Bishop Wolfgang Huber inda a ciki ya yi kashedi game da mayar da Jamus wata ƙasar musulmi. Masanin kimiyyar addinin ya ce abin baƙin ciki shi ne har yanzu al´umar wannan ƙasa sun ƙi amincewa da gaskiya cewar addinin musulunci wani ɓangare na al´umar Jamus. Ya ce ƙungiyarsa ta cike dukkan ka´idojin da suka wajaba na bawa addinin musulunci matsayin wata ƙungiyar jama´a a hukumance. Ya ce hasali ma ba a ɗaukar musulumin da muhimmanci.

To amma Alboga ya yaba da shugaban babban taron Bishop-Bishop na Jamus Archbishop Robert Zollitsch wanda ya fito ƙarara ya goyi da bayan koyar da darussan addinin musulunci. Shi kuwa babban sakataren majalisar tsakiya ta musulmi a Jamus Aiman Mazyek suka ya yi game da rashin amincewa da wannan addini a nan ƙasar. Ya ce tun sama da shekaru 20 da suka gabata ake gwagwarmayar neman izinin koyar da addinin musulunci to amma har yanzu haƙa bai cimma ruwa ba.


4. "´Yancin yin addini ya haɗa da bawa mutum damar tafiyar da rayuwarsa kamar yadda dokin addinisa suka tanadar tare da samar da kyakyawan yanayin kafa cibiyoyi da ƙungiyoyin addini. Amma ba haka ya ke ga gamaiyar musulmi a Jamus ba, duk da gagarumar gudummawar da suke bayarwa na ci-gaban wannan ƙasa kamar sauran takwarorinsu na ƙungiyoyin addinai daban."


Aiman Mazyek ya ƙara da cewa ko da yake babu laifi yadda a kullum ake gabatar da sabbin sharuɗɗa ga musulmi, amma abin baƙin ciki shi ne da zaran sun cike waɗannan sharuɗɗa sai kuma a ƙirƙiro wasu sabbi. Ya ce haka tamkar ana wasa da hankalin musulmi ne a dange da batun ba su ´yanci daidai da sauran mabiya wasu addinai daban.