1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankin Darfur na ci gaba da kasancewa a hali na jalli joga

Ibrahim SaniApril 10, 2006

Kungiyyar tsaro ta Nato , zata kai dauki a yankin Darfur dake Sudan

https://p.dw.com/p/BvTf
Babban sakataren kungiyyar Nato
Babban sakataren kungiyyar NatoHoto: AP

Ya zuwa yanzu dai jami´an Mdd da kuma masu fashin baki nada ra´ayin cewa har yanzu ba a rabu da bukar ba a yankin na Darfur, a game da irin yadda ake take hakkoki na bil adama daga aiyyuka irin na yan tawaye dake cin karen su babu babbaka.

Wannan hali a cewar jami´an ya kara haifar da yanayi na rudani da kaka ni kayi ga alummar yankin, a sakamakon tsaiko da aka samu na aiyyukan jami´an bayar da agajin gaggawa, dake gudanar da aiyukan su a yankin.

A cewar rahotanni ire iren wadannan abubuwamn na ci gaba da wanzuwa ne duk kuwa da kasancewar dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na kungiyyar hadin kann kasashen Africa, a kalla dubu bakwai.

Ya zuwa yanzu dai daga shekaru uku da suka gabata kawo yanzu, an kiyasta cewa dubbannin mutane ne na yankin suka rasa rayukan su ,wasu kuma sama da miliyan biyu suka yi kaura daga yankin don tsira da rayukan su.

Bisa kuwa irin wannan hali da ake ciki,kasar Amurka ta yarda da tura tawagar masu bada shawara daga kungiyyar tsaro ta Nato izuwa yankin na darfur don taikamawa kungiyyar ta Au, wajen dakatar da rikice rikice da tashe tashen hankulan dake faruwa a yankin.

A cewar jaridar washinton Post, jami´an kungiyyar ta Nato da yawan su ya tasamma dari biyar zasu taimakawa kungiyyar ta Au ne da bayanan sirri da kuma sanin makamar aiki, don ganin cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a game da burin da aka sa a gaba.

Wannan yunkuri dai a cewar bayanai na daga cikin matakan share fage ne, kafin a nan gaba Mdd ta aike da babbar tawagar ta ta dakarun kiyaye zaman lafiya izuwa kasar ta Sudan.

YA zuwa yanzu ba a sami tabbaci ba daga babban ofishin kungiyyar ta Nato a game da matakin aikewa da jami´an nata izuwa yankin na Darfur, to amma duk da haka tuni mahukunta a Sudan suka yi watsi da wannan aniya, matukar akwai jami´an Amurka dana kasashen Turai a cikin wannan tawaga.

Idan dai za a tunawa, a can baya kasar ta Sudan ta kekasa kasar kin amincewa da zuwan dakarun sojin Mdd izuwa kasar, wanda daga baya kuma ta sauko daga hawa kujerar nakin da tayi.

Kokarin tura tawagar dai ta Mdd, izuwa yankin na Darfur ya samo asali ne daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, bisa irin yadda ake ci gaba da take hakkokin mata da kana nan yara a yankin , a sakamakon aiyukan kungiyoyin yan tawaye, dake cin karen su babu babbaka a yankin.