1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yankin Scotland na neman ballewa daga Birtaniya

Salissou Boukari
March 28, 2017

A wannan Talatan ce 'yan majalisar dokokin Scotland ke kada kuri'a domin amincewa ko akasin haka da sake wani zaben raba gardama wanda zai basu damar ballewa a lokacin da kasar ke shirin ficewa daga EU

https://p.dw.com/p/2a5Ku
Schottland Brexit Nicola Sturgeon
Hoto: picture alliance/AP Photo/A. Milligan

A ranar Laraba ce dai (29.03.2017) Firaministar Birtaniya Theresa May za ta mika takardar fara aiwatar da shirin ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai a hukumance. Tun dai a ranar Laraba da ta gabata ce ya kamata majalisar ta Scotland wadda masu rajin samun mulkin kai suka fi yawa a cikinta ta yi wannan zama, amma kuma harin da aka kai a majalisar dokokin kasar ta Birtaniya a Westminster da ke birnin London ya sa aka dage batun kada kuri'ar.

Yankin na Scotland dai na adawa da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, wanda a lokacin kada kuri'ar neman ficewa daga Tarayyar ta Turai, yankin ya nuna adawarsa da kashi 62 cikin 100, inda ake ganin idan har suka yi nasarar ballewa,  to za su shiga cikin kungiyar ta Tarayyar Turai matakin da ake gani tamkar wani sare kafafu ga Birtaniya.