1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yansanda sun tarwatsa matasa masu zanga-zanga a birnin Athens ta ƙasar Girka

May 1, 2010

Anan jamus ma dai an ba hammata iska tsakanin masu tarzoma da 'yansanda a lokacin bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a birnin berlin.

https://p.dw.com/p/NCHt
'Yansanda na ɗauki ba daɗi da masu zanga-zanga a Birnin AthensHoto: AP

'Yansanda sunyi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa matasa masu zanga-zanga a birnin Athens na ƙasar Girka a lokacin da ma'aikata dake faretin zagayowar ranar ma'aikata ke wucewa ta gaban ma'aikatan kuɗin ƙasar.

Haka kuma sai da 'yansandan suka harba barkonon tsohuwa akan wasu masu zanga-zanga da suka nemi kai hari wani Otel na alfarma a birnin na Athens.

Anan jamus ma dai an ba hammata iska tsakanin masu zanga-zanga da 'yansanda a lokacin bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a birnin berlin.

Kimanin masu zanga-zanga duba ɗaya ne suka ja daga a wani sashe na birnin Berlin domin adawa da 'yan ƙungiyar dake goyon bayan Haramtacciyar jam'iyar NAZI.

A yayinda  kuma 'yansanda dubu bakwai ke sintiri a birnin baki ɗaya domin hana ɓarkewar bata kashi tsakanin ɓangarorin biyu.

A birnin Hamburg dake arewacin Jamus 'yansanda sun kame wasu masu tarzoma da suka kai hari akan ofisoshin 'yansanda tare kuma da cinna wuta a guraren zuba shara.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza sadissou Madobi