1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan´uwa musulmi sun lashe karin kujeru 28 a zaben majalisar dokoki a Masar

November 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvJB

Jam´iyar adawa ta ´yan´uwa musulmi a kasar Masar ta yi ikirarin lashe karin kujeru 28 a zagayen kusa da na karshe na zaben ´yan majalisar dokoki da aka gudanar a jiya asabar. Wani mai magana da yawun jam´iyar ya ce nasarar ta nuna irin karfin da jam´iyar ta ´yan´uwa musulmi ke samu. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce ´yan sanda sun hana a kada kuri´a a wurare da dama inda jam´iyar ´yan´uwa musulmi ta tsayar da ´yan takara. To sai dai kakakin ma´aikatar harkokin cikin gida ya ce ´yan sanda sun tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana ne. Wani dan jarida na ketare ya ce an tursasa masa sannan an kwace masa kayan aiki.