1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yar takarar shugabancin kasa a Somaliya

November 22, 2016

Fadumo Dayib mazauniyar kasar Finland a yanzu ta koma kasarta ta Somaliya domin tsayawa takarar shugabancin kasa, ta zama kallabi tsakanin rawuna, ta na takara da maza 26.

https://p.dw.com/p/2T4Oj
Portrait Fadumo Dayib
Hoto: Chris Schwagga

Ba ya yiwuwa dai a gudanar da zabe kai tsaye a Somaliya a yanayin mai sarkakiya da kasar ke ciki, saboda har yanzu ba'a kawo karshen yaki a kasar ba. A ranar 30 ga wannan watan na Nuwamba ne majalisar dattijai da ta wakilai za su zabi sabon shugaban kasa. Sai dai kuma tuni ake ta dage ranar zaben, mai yiwuwa sai wani lokaci a nan gaba.

Fadumo Dayib mai shekaru 44 'yar kasar Somaliya na so ta zama shugabar kasa mace ta farko a gwamnatin kasar, abin da wasu 'yan kasar ke ganin abin ci gaba ne, sai dai ba duka su ka santa ba kasancewar sauran 'yan takarar 24 dukkaninsu maza ne. Da aka tambaye ta ko ta na alfahari a ganin ita ce mace wadda ke son yin takarar shugabancin kasa:

" Na yi mamaki, amma ba alfahari ba. Ina jin cewa na san mutane da dama wadanda ke shiga shafukan sada zumunta, wasu ba su san ko ni wacece ba, galibin 'yan Somaliya sun san mutanen da ke fita yakin neman zabe ne, yin hira a gidajen radiyo da kiran mutane wajen yakin neman zabe, mutane suna mamaki duk ba na wannan."

Harvard University Fadumo Dayib
Fadumo Dayib ta kasance mai hangen makoma ga SomaliyaHoto: Harvard University/Stephanie Mitchell

Fadumo za ta ci gaba da kasancewa bakuwa ga 'yan Somaliya da dama idan dai ba wani kokari ta yi ba. A watan Oktoba ne ta koma Mogadishu daga kasar Finland inda ta shafe shekaru 26 ta na zaman gudun hijira, dalili kuwa shi ne yakin basasa, wanda kuma har yanzu ba'a kawo karshensa ba, saboda kuwa har yanzu a kullum ana aikata kisan gilla. Tsaron lafiyar Fadumo da ma sauran 'yan takara lamari ne babba. Fadumo ta na zaune ne a wani Otel mai cikakken tsaro.

Fadumo dai ta san irin kasadar da ke tattare da abin da ta tunkara da kuma tsadar da hakan ya ke da shi na neman takarar shugabancin Somaliya. Da ta so ta na iya zamanta a Finland tare da iylanta da 'ya'yanta hudu, inda ta ke aiki a matsayin jami'ar lafiya ta na kuma da digiri na biyu a fannin sha'anin mulki. A yanzu kuma ta na rubuta kundin digirinta na uku a kimiyyar siyasa.

Somalia Autobombe in Mogadischu
Kai hare-hare a Somaliya ya zama ruwan dareHoto: Getty Images/AFP/M. Abdiwahab

Ta ce dai ta shiga takara ce saboda ta na ganin wani hakki ne da ya kamata ta sauke wa wuyanta ta taimakawa cigaban kasa, ta jira tsawon shekaru 26 domin samun shugaba nagari mai kishin al'ummar Somaliya da kasar Somaliya, babu alamun samuwar hakan.

Fadumo ta kwan da sanin cewa ba za ta samun wannan dama ta shugabancin kasa da ta ke muradi ba, saboda sarkakiyar matsalolin tsaro da kasar ke fama da su, majalisar dokoki ta gaba da ma shugaban kasa, ba jama'a ne za su zabe su kai tsaye ba, sai dai ana zaben ne ta hanyar wakilai. Shugabannin al'ummomi a kasar su na taka gagarumar rawa wajen nadin. A tsarin gargajiya na Somaliya a yanzu mace ba ta da damar samun shugabanci. Musamman ma ga Fadumo wadda ke da ra'ayin rushe tsarin hauloli.

" Wannan tsari ne mai cike da cin hanci da magudi, tsari ne wanda bai yarda da gogayya ko kwarewa ba, baya kuma son mutane masu kwazo da hazaka da kishin kasa, tsari ne kawai na maza wadanda su ke gani su ne kadai su ka iya."

Mai yiwuwa dai Fadumo na fatan zabe na gaba na dimokradiyya, abu ne mai yiwuwa yanzu,  ko kuma watakila ta iya samun dama a shekara ta 2020