1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara miliyan shida na rasuwa a Afrika

November 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvK1

Yara kusan miliyan shida ne a kasashe dake fama da sahara a Africa ke rasa rayukan su a kowa ce shekara a sakamakon yunwa da kuma rashin cin abin ci mai gina jiki.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin rahoton shekara na hukumar bunkasar Abinci ta Mdd.

Bugu da kari rahoton ya kuma yi nuni da cewa da yawa daga cikin yaran na rasuwa ne a sakamakon cututtuka irin su malaria da kyanda da kuma ciwon sanyi.

Har ila yau rahoton ya kuma tabbatar da cewa matsalar talauci da rashin ilimi da kuma cututtuka na daga cikin abubuwan dake haifar da yawan mace mace a tsakanin yara a kasashe masu tasowa.

A karshe rahoton yayi tsokaci da cewa dole ne sai an kara kaimi wajen kokarin ganin an kau da yunwa daga doron kasa ta hanhyar noma abinci wadatacce.