1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Yemen na ci gaba da shiga halin tasku

Lateefa Mustapha Ja'afarOctober 21, 2015

Asusun kula da ilimin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya yi gargadin cewa rashin tsabtataccen ruwan sha da kuma muhalli a Yemen na gaf da janyo illa ga yaran kasar.

https://p.dw.com/p/1Gs9Y
Halin da kananan yara ke ciki a kasar Yemen
Halin da kananan yara ke ciki a kasar YemenHoto: Reuters/K. Abdullah

UNICEF din ta kara da cewa matsalar za ta haifar da rashin abinci mai gina jiki da kuma cututtuka ga kananan yaran 'yan kasa da shekaru biyar a kasar. Kawo yanzu dai sama da mutane 5,500 ne suka hallaka tun bayan da Saudiya ta kaddamar da kai hare-hare ta sama tare da tallafin sauran kawayenta kasashen Larabawa a Yemen din. Cikin watan Maris din da ya gabata ne dai Saudiyan ta fara jagorantar rundunar taron dangin kasashen Larbawan wajen kai wa ksar ta Yemen da ke fama da dunbin talauci hare-hare ta sama, a wani mataki da ta kira da kokarin fatattakar 'yan tawayen Houthi da ke zaman Musulmi mabiya shi'a wadanda suka kwace iko da babban birnin kasar Sanaa.