1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniya tsakanin Jamus da Syria

August 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuCl

Jamus da Syria sun rattaba hannu ,akan yarjeniyar taimakon raya ƙasa, a sakamakon ziyara aikin da ministar kulla da taimakon raya ƙasa ta Jamus Heid-Marie Wieckzoreckzeul ta kai a kasar Syria.

A wannan yarjeniyar Jamus ta taimakawa Syria da tsabar kuɗi Euro milion 32, wanda hukumomin Damascus za su anfani da shi ta fannin samar da tsabttatun ruwan sha ga jama´ar ƙasa.

A wani fannin kuma, Jamus ta ware kuɗi Euro MiIlion 4 ga Syria, domin gina makarantu ga yan gudun hijira Irak da su ka samu matsuggunai a kasar.

Hed-Marie Wieckzorek-Zeul ta bayyanawa hukumomin Syria dalilan da su ka sa Jamus ta bada wannan tallafi.

Ministar taimakon raya ƙasa ta Jamus, ta gana da shugaban ƙasa Bashar AL Asad, da Paminista Mohamed Naji Otri.

Gobe idan Allah ya kai mu, za ta kammalla wannan ziyara ta kwanaki 3.