1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya

Sadissou YahouzaMay 29, 2010

Ƙasashen duniya sun cimma sabuwar yarjejeniyar matsa ƙaimi da kuma sa ido domin hana yaɗuwar makaman nukiliya

https://p.dw.com/p/NcZp
Tutar Hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nukiliya

Ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya a duniya, sun cimma daidaito kan wani saban mataki na matsa ƙaimi da sa ido,domin mutunta wannan yarjejeniya.

Saban matakin ya ƙalubalanci Ƙasashe biyar na duniya da suka mallaki manyan makamann  nukiliyar wato Amurika, Rasha,China, Fransa da Britaniya da su rage yawan wannan makamai.A ɗaya wajen, ƙasashen sun amince suyi aiki kafaɗa da kafaɗa, domin tsarkake yankin Gabas ta tsakiya daga makaman nukiliya, saboda haka,sun ƙuduri aniyar shirya taro na mussamman  a shekara ta 2012 kan batun.Sannan sun yi kira da babbar murya ga ƙasashen Isra´ila, Indiya, Pakistan da Koriya ta Arewa, suma su rattaba hannu akan yarjejeniya hana yaɗuwar makaman nukiliya da suka ƙauracewa.