1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar shawo kan rikicin Siriya ta sulhu

Gazali Abdou TasawaDecember 19, 2015

Illahirin kasashe15 mambobin komitin sulhu da suka hada da Rasha suka kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar wanda ya tanadi bin hanyar sulhu wajen shawo kan rikicin kasar ta Siriya.

https://p.dw.com/p/1HQOB
Syrien-Resolution in New York verabschiedet
Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisar Dinkin Duniya ta sanya hannu kan wani sabon daftarin doka wanda ya sanya kira zuwa ga tsagaita wuta a yakin kasar Siriya. Illahirin kasashe15 mambobin komitin da suka hada da kasar Rasha ne suka kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar wanda ya kuma tanadi bin hanyar sulhu wajen shawo kan rikicin kasar ta Siriya.

Sai dai kuma sabon daftarin ya sake jaddada bukatar ganin makomar kasar Siriya ba tare da Shugaba Bashar Al-Assad ba. Ministan harakokin wajen Faransa Lauren Fabius ya bayyana cewa wannan yarjejeniya tana cike da kyakyawar fata sai dai tana bukatar samun tabbacin ficewar Shugaba Bashar al-Assad daga karagar milkin kasar domin ba ta yiwuwa a ce za a hada kan 'yan kasa a karkashin jagorancin wani shugaba da ya yi faman kisan al'ummarsa. Kuma matsawar Shugaba Bashar al-Assad zai ci gaba da nacewa kan mulki to sasanta 'yan kasar Siriya zai wahala.