1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnati da yan tawayen RCA

February 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuSU

An cimma sabuwar yarjejeniyar sulhu, tsakanin dakarun gwamnati da yan tawayen Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

An rattaba a kan yarjejeniyar, a birnin Tripolin ƙasar Lybia, bisa jagorancin shugaba Muhammad Khadafi, tare da halartar takwaran sa, Fransois Buzize na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Ɓangarorin 2, sun alƙawarta kawo ƙarshen rikicin tawaye a wannan ƙasa, da a ka daɗe a na gwabazwa, sannan za su belin dukan pirsinonin da ke cikin hannun su.

Bugu da kari,Gwamnati ta yi alkawarin baiwa shugabanin tawaye da ke gudun hijira, damar komowa gida, ba tare da fargaba ba.

Shugaban ƙasar Libya, ya yi kira ga ɓangarorin 2, sun cika alƙawarin da su ka ɗauka.