1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar sulhu tsakanin yan tawaye da gwamnatin Mali

July 4, 2006
https://p.dw.com/p/Burc

Sanarwar daga Algers babban birnin Algeria, ta ce, an rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lahia, tsakanin yan tawaye da gwamnatin ƙasar Mali.

A cimma wannan mataki, tare haɗin gwiwar gwamnatin Alegria, da ta shiga tsakani.

Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata yan tawayen ƙasar Mali, sun kai hare hare, a yankin Kidal, inda su ka yi awan gaba, da makama da kuma dukiyoyi masu yawa.

Daga jerin buƙatocin su, yan tawaye sun nemi gwamnati ta kauttata makomar yankin su, sannan a ƙara masa cikkaken yanci.

Bayan kwanaki na shawarwari, sanarwar da aka bayana a yau, ta ce yan tawayen sun yi watsi da buƙatar yancin gashin kan Kidal.

Sannan a nata ɓangaren gwmanati, ta alƙawarta saka kuɗaɗe masu yawa, domin kauttata rayuwar al´ummomin kidal.

Bayan hare haren na watan da ya wuce, al´ummomin ƙasar Mali,, sun shiga zullumin sake ɓarkewar rikicin tawaye, irin wanda ya abku a shekarun1990.