1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

yarjejeniyar sulhu tsakanin yan tawayen gabacin Sudan da gwamnati

June 20, 2006
https://p.dw.com/p/ButA

A yammacin jiya ne, babbar jama´iyar Sudan mai riƙe da ragamar mulki ta ƙaddamar da wani taron gangami abirnin Khartum, wanda ya samu halartar shugaban kasa Omar El beshir.

A cikin jawabin da ya gabar, Omar El Beshir, ya bayyana gamsuwa da yarjeniyoyi daban-daban,da a ka cimma tsakanin yan tawaye, da gwamnati.

An shirya taron, ranar da yan tawayen gabacin ƙasar da gwamnati su ka amice da tsagaita wuta, bayan wata da watani na tantanawa.

Saidai a wani sashen kuma, shugaban ƙasar Sudan, ya jaddada matsayin gwamnatin sa, na yin watsi da batun tura dakarun shiga tsakani,na Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfour.

Ya ce, yayi rantsuwa da mahallici , muddun ya na bisa karagar mulkin Sudan, babu batun aika tawagar Majalisar Sinkin Dunia a Darfour, domin,Soudan itace ƙasar farko a kudancin Sahara da ta samu yanci, daga turawan mulkin mallaka,a yanzu kuma, ba zata amince ba, ta koma ƙarkashin wanni saban mulkin mallaka inji shugaba El Beshir.