Yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Sudan da ´yan tawayen JEM.
February 24, 2010Talla
Gwamnatin Sudan ta rattaba hannu kan yarjejeniya tare da
ƙungiyar ´yan tawayen Justice and Quality Movement wato
JEM a ɓirnin Doha. Wannan yarjejeniya za ta bai wa ƙungiyar ´yan tawayen damar raba madafun iko da gwamnati.
Doka ta ukku da wannan yarjejeniya ta ƙunsa ta nunar da
cewa gwamnatin Sudan da yan tawayen JEM sun yarda a
dama da ƙungiyar yan tawayen ta JEM a dukan matsayi na iko.
Sai dai wannan yarjejeniya ta nunar da cewa a nan gaba ne
bangarorin biyu za su amince da wannan doka da aka rattaba
hannu a kanta a Doha, babban ɓirnin Katar.
A bayanin da Anja Dargatz, wakiliyar asusun Friedrich Ebert
da ke ɓirnin Khartum game da yarjejeniyar cewa ta yi da farko
wajibi ne mu yi bayani cewar ba maganar wata yarjejeniya ce
ta zaman lafiya ba, sai domin a albarkaci wata yarjejeniya ce
ta ajiye makamai, wadda aka cimma daidaituwa kanta a Chadi
ranar asabar da ta wuce, wadda kuma a yanzu aka ɗaga
matsayinta zuwa rukunin shawarwarin sulhu na Doha. JEM dai
ta yi nuni da cewar wannan wani mataki ne na farko game da
kwance damarar makamai, amma kuma dole ne gwamnati ta
nuna alkiblar da ta fuskanta. A saboda haka gaba daya
magana ce ta neman kusantar juna tsakanin sassan biyu,
amma ba wata yarjejeniya ce ta zaman lafiya ba.
Dokar dai ta buƙaci ɓangarorin biyu da su amince da JEM a
matsayinta na babbar ƙungiyar 'yan tawaye a Sudan da ta
cenja zuwa jam´iyar siyasa. Wadda ke nan ƙungiyar ta JEM za
ta kasance jamiyar siyasa da zaran an rattaba hannu a kan
kamalalliyar yarjejeniyar nan ta ranar 15 ga watan Maris mai
zuwa kafin zaɓen da zai gudana a ƙasar ta Sudan a watan
Afrilu ,wanda shi ne zaɓe irinsa na farko cikin shekaru 24 da
suka gabata.
A ranar asabar da ta gabata sai da wakilan gwamnatin Sudan
da na yan tawayen suka sa hannu a kan daftarin wannan doka
a ƙasar Chadi suna masu shelar tsagaita buɗe wuta a rikicin
lardin Darfur da aka shafe shekaru bakwai ana fuskanta. Sun
kuma yarda su kadammar da tattaunawar gaggawa domin
cimma yarjejeniyar da kuma haɗe mayakan JEM da sojoji da
yan sandan ƙasar ta Sudan.
Shugaban Sudan Omar Hassan Albashir ya je ɓirin Doha tare
da shugaban JEM Kamal Ibrahim. Shugaba Idris Deby na Chadi
da sarkin Katar Sheikh Hamad Bin Khalifa al-Thani wanda
ƙasarsa ta ɗauki dawainiyar gudanar da tattaunawa tsakanin
gwamnatin Sudan da yan tawayen su kuma sun halarci
wannan taro.
Ko kafin shiga wannan taro Shugaba Albashir ya yi jawabi
inda ya kira yarjejeniyar ta zaman lafiya tamkar matakin farko
na kawo ƙarshen rikicin lardin Darfur tare da kyautata fatan
cewa za a cimma kyakkyawar yarjejeniya a wannan lardi na
yammacin Sudan kafin gudanar da zaɓe.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, mutane dubu ɗari ukku
suka rasa rayukansu a rikicin na yankin Darfur a baya ga
wasu su miliyan biyu da ɗari bakwai da suka rasa
matsugunansu.
Mawallafi: Hussaina Jibril Yakuba
Edita.: Ahmed Tijani Lawal
Talla