1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YARJEJENIYAR ZAMAN LAFIYAR CÔTE D'IVOIRE - WAI SHIN ZA TA AIWATU KUWA ?

YAHAYA AHMEDApril 7, 2005

Mayakan juna a kasar Côte d’Ivoire sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu, bayan taron kwana uku da suka yi a birnin Pretoria na kasar Afirka Ta Kudu. Bisa dukkan alamu dai, za a huskanci matsaloli nan gaba, saboda har ila yau ba a tattauna batun da ke hana ruwa gudu a yunkurin samad da zaman lafiya a kasar ba – wato na cancantar tsayawa takarar zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/BvcX
Magoya bayan shugaba Gbagbo yayin da suke zanga-zanga a kan titunan birnin Abidjan.
Magoya bayan shugaba Gbagbo yayin da suke zanga-zanga a kan titunan birnin Abidjan.Hoto: AP

A zayyane dai, an cim ma yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Pretoria, tsakanin bangarorin da ke yakan juna a kasar Côte d’Ivoire. Amma wai shin, wannan yarjejeniyar za ta aiwatu kuwa ? Duk bangarorin biyu, za su iya kiyaye ka’idojin yarjejeniyar, ba tare da daya daga cikinsu ya fara zargin dayan da saba musu ba ? Yarjejeniyar da aka cim ma a cikin shekara ta 2003 dai, ba ta yi karko ba, saboda ko wanne daga abokan hamayyar biyu na ganin kansa ne kamar a sama da doka yake.

Tun da mayakan saman Côte d’Ivoire din, suka kai hari kan rukunan sojojin Faransa da ke aiki karkashin laimar Majalisar dinikin Duniya ne, aka shiga cikin wani hali na mulkin rudu a kasar. Kwatsam, sai ga shi kungiyar nan da ke kiran kanta "matasa `yan kishin kasa", wadda ta kunshi gungun `yan daba masu nuna biyayya ga shugaba Laurent Gbagbo, ta tunzura `ya`yanta ta da tarzoma a kan titunan birnin Abidjan. A wannan lokacin, Faransawa da yawa ne suka tsallake rijiya da baya, wajen ficewarsu daga kasar. Tabarbrewar halin tsaron da kasar ta sami kanta a ciki bai canza ba har zuwa yanzu. Gidajen rediyo da jaridun da ke karkashin gwamnati kuma, ba su daina tunzura al’umman kasar su afka wa baki ba, musamman ma dai Faransawa.

A bangare daya kuma, shugaba Gbagbon na ganin kansa ne kamar wani jarumi, wanda shi kadai ne zai iya kubutad da kasarsa zuwa samun cikakken `yancinta.

To bayan wannan yarjejeniyar da aka cim ma a birnin Pretoria, wai da akwai wani abin da zai sake a kasar ? Bisa yadda al’amura suke a yanzu dai, za a iya amsa wannan tambayar da a’a. Ko wane bangare zai koma ramin kurarsa ne ya sake jan damarar ko da ta kwana. `Yan kungiyar "matasa masu kishin kasa" na nan da shiri; abin da suke jira ne kawai umarni daga shugaba Gbagbo, sai su shiga aikinsu na gallaza wa al’umma. Babu dai wani aikinsu da ke alamta kishin kasa. A halin yanzu, babu abin da ya fi wa `yan siyasa muhimmanci a kasar tamkar su zarce suna rika da madafan iko. A cikin watan Oktoba mai zuwa ne za a yi zabe a kasar, na zaban shugaban kasa da kuma sabuwar Masjalisa.

Babbar matsalar da ke hana ruwa gudu tsakanin `yan tawayen da wadanda ke jan ragamar mulki a kasar, ita ce wani babi na kundin tsarin mulkin kasar, mai lamba 35. A wannan babin dai, an rubuta cewa, babu wanda ya cancanci ya tsaya takarar zaben shugaban kasa, sai ya kasance mahaifiyarsa da ubansa ma a kasar Côte d’Ivoire din aka haife su. Wannan kuwa, wani babban kaye ga jam’iyyun adawar, wadanda dan takaransu, Alassane Ouattara, aka hana shi tsayawa a zaben. Bugu da kari kuma, wannan babin na kundin tsarin mulkin, ya mai da ko wane mutum daya bisa uku na saniyar ware. Kusan rabin duk `yan kasar dai na da iyaye baki, wadanda aiki ne ya kawo su Côte d’Ivoire din har suka hayayyafa. Amma wannan batu mai muhimmanci, ba a tabo shi ba a tattaunawar kulla yarjejeniyar ta Pretoria; to ta yaya ne kuwa za a kyautata zaton cewa, `yan tawayen za su kwance damara ?Wato a nan dai, za a iya cewa yarjejeniyar ba za ta iya janyo zaman lafiya mai dorewa ba.

Al’amuran da suka wakana a fagen siyasar kasar, a `yan watannin bayan da suka wuce ma na nuna haka. Wani rahoton da Majalisar dinkin Duniya ta buga a kan kasar na kakkausar suka ga salon keta hakkin dan Adam da ke ta yaduwa. Rahoton dai na zargin duk bangarorin biyu ne, wato `yan tawaye a arewacin kasar, da kuma `yan tsagerun kudu da ke samun daurin gindin gwamnati.

A cikin wannan halin ne dai Majalisar dinkin Duniyar, ta kara wa’adin girke dakarun kare zaman lafiyarta dubu 6 da ke kasar, wadanda kuma sojojin Faransa dubu 4 ke karfafa wa gwiwa. A karshen shekarar bara ne kuma, kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniyar, bayan ya yi ta tafiyar hawainiya, ya sanya wa kasar takunkumi, wanda ya kunshi hana sayar mata da makamai da kuma hana manyan jami’an gwamnatin Laurent Gbagbo, da shi ma shugaban da kansa da kuma na `yan tawayen fiita zuwa ketare.

A zahiri dai, masu jan akalar harkokin siyasa a kasar ba su damu da makomarta ba. Hakan kuwa, wani babban cikas ne ga samun nasarar aiwatad da yarjejeniyar ta Pretoria, wadda da ma can saboda angaza wa bangarorin biyu da Majalisar dinkin Duniya da kuma kungiyar Taryyar Afirka suka yi ne, ya sanya su duka rattaba hannu a kanta.