1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zamna lahia tsakanin gwamnati da yan tawayen gabacin Sudan

October 10, 2006
https://p.dw.com/p/BugO

Gwamnati da yan tawayen gabacin Sudan, sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsaigaita wuta, a birnin Asmara na ƙasar Erythrea.

Saidai ya zuwa yanzu, ba a bayyana matakan da wannan sulhun ya tanada ba.

Tun watan satumber da ya wuce, ɓangarorin 2, su ka cimma daidaito, a kan batun ajje makamai, tare da alƙawarta ci gaba da tantanwa, domin kawo ƙarshen rikicin ,da ya ɗauki tsawn shekaru 10.

Sakatare Jannar na rundunar yan tawayen gabacin Sudan, Mubarack Mubarack Salim, ya shaidawa manema labarai cewa, yarjenejiyar ta tadani saka kuɗaɗe masu yawa, domin kyautata rayuwar al´umomin yanki gabas, da ke fama da ƙazamin talauci.